fidelitybank

Sojoji sun ragargaji ‘yan ta’adda a tafkin Chadi

Date:

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta tabbatar da kashe ƴan bindiga da dama a Parisu, kusa da dajin Sambisa sakamakon hare-haren da ta kai, ta kuma kai makamancin harin a Tumbun Agiri da ke Tafkin Chadi.

Rundunar sojin saman cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi ta ce ta samu nasara sakamakon haɗin gwiwa daga sojojin da ke aiki ƙarƙashin rundunar Hadin Kai da ke jihar Borno, a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin rundunar sojin saman, Edward Gabkwet ya ce a ranar 5 ga watan Janairu ne aka kai samamen na Parisu yayin washe garin ranar kuma, sojoji suka far wa ƴan bindigar da ke Tafkin Chadi.

A cewar rundunar, an kashe ƴan bindiga 12 a Parisu sannan an lalata kayayyakin aikinsu lamarin da ya rage musu ƙarfi wajen kai hari ko haɗa runduna ta kansu.

Dangane da samamen da aka kai a Tafkin Chad kuma, rundunar ta ce hare-haren da aka akai sun lalata motoci da baburan ƴan bindigar tare da kashe wasu daga cikinsu da dama.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp