fidelitybank

Sojoji sun ragargaji ‘yan ta’adda 10 a Katsina

Date:

Rundunar sojin Kasa ta Hadarin Daji, ta kai wa ‘yan ta’adda farmaki tare da kubutar da mutum tara da aka yi garkuwa da su, sun kuma gano makamai da albarusai, da babur da na’urorin sadarwa.

A ranar 3 ga watan Junairu 2024, runduna ta takwas ta sojin Najeriya ce ta yi wannan aikin karkashin jagorancin Manjo Janar Godwin Mutkut, a karamar hukumar Batsari da Safana da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya inda aka kashe ‘yan ta’adda 10 yayin da wasu da dama suka tsere da munanan raunuka.

Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce ta samu bindiga kirar AK-47, da alburusai da bindigogi kirar gida guda uku da harba-ruga bakwai da sauran da sauran bindigogi masu hatsari da na’urorin sadarwa da wayoyin hannu da kakin soji tare da babura hudu.

Haka kuma sanarwar ta ce a wannan ranar ce dai kuma dakarun soji na rundunar HADARIN DAJI da ke aiki a jihar Zamfara suka kai samame kauyukan Dansadau da Dandalla a karamar hukumar Maru, inda suka kubutar da mutum tara da ake garkuwa da su da suka hadar da mata biyar da jarirai hudu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ‘yan bindigar sun gudu ne suka bar mutanen bayan musayar da jami’an tsaro.

Tuni aka sada mutanen da iyalansu a garin Magami kamar yadda sanarwar ta bayyana.

vanguard news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp