Rundunar sojin Najeriya ta ce ta hallaka wasu ƴan bindiga 21 a dajin Shawu a karamar hukumar Faskari na jihar Katsina.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, ta ce dakarunta na Operation Fansan Yamma ne suka samu nasarar kashe ƴan bindigar bayan kai musu hari a maɓoyarsu ranar 23 ga watan Mayu, a ci gaba da yaƙi ayyukan ɓata-garin.
Sanarwar ta ce an samu nasarar kashe ƴan bindigar ne bayan artabu na tsawon lokaci, ciki har da waɗanda kogi ya tafi da su lokacin da suke ƙoƙarin tserewa.
Sai dai sanarwar ba ta bayar da rahoton mutuwar wani jami’in soji ba a artabun da aka yi.
Ta kuma ce an ƙwato mamakai da harsasai da dama – ciki har da babura 40 da shanu da dama waɗanda ƴan bindigar suka sace.
Har ila yau, sojojin sun ce samamen da suka kai ya sa ƴan bindigar tserewa tare da barin sansaninsu, inda suka fantsama cikin dazuka.