Rundunar hadin gwiwa da ta kunshi sojojin Najeriya da na ruwa, a ranar Asabar din da ta gabata sun kai samame wani sansani na wasu ‘yan bindiga da suka addabi yankin Aguata/Orumba na jihar Anambra.
POLITICS NIGERIA ta tattaro cewa, sansanin da ke Aguluezechukwu a cikin karamar hukumar Aguata ta jihar, jami’ansu sun yi awon gaba da su tare da kama wasu da dama.
An kwato kayayyaki da dama da suka hada da kayan abinci, motocin sata da kuma layu masu yawa.
Har ila yau sansanin na dauke da wani wurin ibada wanda masu laifin ke amfani da shi wajen shirya laya da kuma rantsuwar sirri. Jami’an sun kuma kona wata babbar mota kirar Bulldozer da aka yi amfani da ita wajen tare kofar shiga sansanin. domin kare ta daga hare-hare.
An kafa wannan rundunar hadin guiwa ne sakamakon kokarin da gwamnatin jihar ke yi na maido da zaman lafiya a jihar tare da kawar da masu aikata miyagun laifuka da ke son ganin jihar ba za ta iya rayuwa ba.
Ana kyautata zaton ‘yan wannan kungiyar ne da ba a san ko su waye ba ne suka kai harin a shelkwatar karamar hukumar Aguata da kuma hedikwatar karamar hukumar Nnewi ta Kudu.