Rundunar sojin Najeriya ta ce jita-jitar yiwuwar juyin mulki da aka yi wa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu “labari ne na karya”.
Jami’an tsaron fadar shugaban kasa a cikin “high alert” saboda zargin yunkurin juyin mulki a Najeriya.
Rahoton ya ce ana sa ido a kan wasu manyan birged a yayin da kwamandan rundunar tsaron shugaban kasa, Kanar Adebisi Onasanya ya gana da Tinubu da shugaban ma’aikatan sa, Femi Gbajabiamila.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta nakalto daya daga cikin irin wadannan rahotanni a shafinsu na X inda suka rubuta “LABARAN KARYA”.
An dai shiga tada jijiyoyin wuya a Najeriya yayin da ake fama da tabarbarewar tattalin arziki, hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa biyo bayan cire tallafin man fetur da kuma yawo da Naira da shugaba Tinubu ya yi.
A makon da ya gabata ne babban hafsan sojin kasa, Janar Christopher Musa ya yi gargadi game da kiraye-kirayen juyin mulki, ya kuma bukaci jama’a da su guji irin wannan.