fidelitybank

Sojoji sun lalata wak3n ƙera abubuwan fashewa a Borno

Date:

Rundunar sojin saman ƙasar nan ta ce, ta lalata wani sansani da take zargin mayaƙan Boko Haram na ƙera abubuwan fashewa a tsaunukan Mandara da ke jihar Borno.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce, sakamakon yadda a baya-bayan nan mayaƙan Boko Haram ke amfani da abubuwan fashewa wajen kashe fararen hular da ba su ji ba su gani ba, musamman a jihar Borno, ya sa jami’anta suka tsananta bincike domin gano inda mayaƙan ƙungiyar ke ƙera abubuwan fashewar.

..Asalin hoton,NAF/X
Sanarwar ta ce wasu bayanan sirri da sojojin suka samu sun bayyana mata cewa akwai wata masana’anta da ake ƙera abubuwan fashewar da kuma adana su a tsaunin Mandara.

Sojojin saman na Najeriya sun ce bayanan sun tabbatar mata cewa an sauya wa masana’antar matsuguni daga Gwoza zuwa Timbuktu a dajin Sambisa kafin dagabisani a mayar da shi yankin Grazah da ke tsaunin Mandara.

”Sakamakon tsananta hare-hare kan mayaƙan da sojoji ke yi a baya-bayan nan ya sa aka mayar da ɗauke masana’antar daga dajin Sambisa zuwa tsaunukan na Mandara”, in ji sanarwar sojojin.

sojojiAsalin hoton,NAF/X
Sojojin sun ce sun shafe tsawon makonni suna sanya ido kan wurin ƙera abubuwan fashewar da sauran ayyukan mayaƙan a yankin.

”A lokacin da muka ƙaddamar da harin, mun hangi wasu manyan motocin dakon makamai guda biyu a kusa da masana’antar, tsaye ƙarƙashin bishiya”, in ji sanarwar.

”Hakan ne ya sa ba mu yi wata-wata ba muka ƙaddamar da hare-hare a yankin, da nufin lalata masana’antar tare da kashe mayaƙan ƙungiyar”.

Sanarwar ta ci gaba da cewa sojojin sun samu nasarar lalata masana’antar.

Hotunan bayan harin sun nuna yadda wurin ya turnuƙe ta hayaƙi, bayan da masana’antar ta ƙone tare da motocin dakon makaman guda biyu

network news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp