Rundunar soji ta ƙasa, ta ce, ta ceto wasu ‘yan matan sakandiren Chibok biyu, tare da karin wasu mutum 99 daga sansanonin ‘yan ƙungiyar Boko Haram.
A wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Maiduguri babban kwamandan rundunar hadin gwiwwa ta Operation HADIN KAI, Manjo Janar Waidi Shaibu, ya ce dakarun nasu sun kubutar da mutanen ne a sassa daban-daban na jihar.
Gidan Talbijin na Channels TV, ya ruwaito cewa ‘yan matan Chibok din da aka kubutar su ne Rejoice Sanki, mai shekarar 24, wadda aka kubutar tare da ‘ya’yanta biyu, sai kuma Yagana Poly, ita ma mai shekara 24, wadda ita kuma ke da ‘ya’ya hudu.
Sauran mutane 99 da aka kubutar tare da ‘yan matan sun hadar da mata 47 kamar yadda dakarun sojin suka bayyana.


