fidelitybank

Sojoji sun kubutar da ‘yan mata 50 da ake yin karuwanci da su

Date:

Rundunar sojin ruwa ta ce, ta samu nasarar kubutar da ‘yan mata 50, wadanda ta yi zargin cewa an tilasta musu shiga karuwanci a wasu gidajen karuwai biyu a birnin Fatakwal da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Jaridar The CableĀ a Najeriya ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na sansanin sojin ruwa da ke jihar Richard Iginla, na bayyana cewa a yayin samamen sun kama mutum uku da suke zargi da safarar ‘yan matan -wadanda wasunsu shekarunsu ba su fi 14 ba – domin tilasta musu yin karuwanci.

Ya ce Sun kaddamar da samamen ne tare da hadin gwiwwar hukumar yaki da safarar bil-adama ta kasar wato (NAPTIP) da kuma rundunar tsaro da Civil Defence.

Ya ci gaba da cewa ”Mun samu bayanan sirri daga hukumar NAPTIP, wadda ta dade tana bibiyar gidajen karuwan da ake tilasta wa mata galibinsu ‘yan mata yin karuwanci. Daga nan sai muka shirya rundunar hadin gwiwwa cikin gaggawa muka kuma samu nasarar kubutar da wadannan mata”.

hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ę“ansandan jihar Kaduna, sun buʙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ʙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ā€˜Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ʙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ā€˜yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp