Dakarun tsaro na kasa, sun kubutar da mutum bakwai a hannun ‘yan fashin daji a jihar Kaduna.
Dakarun na Operation Forest Sanity, sun yi nasarar kubutar da fararen hula bakwai lokacin da wani aikin sintiri a tsakanin yankunan Birnin Gwari zuwa Chikun.
Wata sanarwa da Kwmashinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya ce mutanen da aka kubutar sun hadar da wata mata da ‘ya’yanta hudu.
A cewarsa, tuni gwamnatin jihar ta damka mutanen hannun makusantansu.
Sameul Aruwan ya ce dakarun tsaron sun yi nasarar kubutar da mutanen ne lokacin da suke sintiri a kan titin Birnin Gwari zuwa Gayam zuwa Kuriga zuwa Manini.
Ya ce ‘yan fashin daji sun bude musu wuta, inda su kuma suka mayar da martani nan take tare da murkushe maharan, wadanda suka tsere cikin daji.