Rundunar sojin Najriya ta ce dakarunta da aka tura don daƙile ayyukan ƴan ta’adda a yankin arewa maso yamma sun yi wa wasu ‘yan bindiga kwantan-ɓauna, tare da kashe biyu daga cikinsu a jihar Kaduna.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojan Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce samamen da suka kai ranar Asabar, 13 ga watan Afrilu 2024, ya biyo bayan samun bayanai cewa an ga ‘yanbindigar suna safarar wani buhu mai dauke da makamai.
Sojojin sun kai samamen ne a kauyen Rafin Sariki da ke karamar hukumar Giwa na jihar.
“Dakarun mu sun yi artabu da ‘yan bindigar, kafin daga bisani su samu nasarar kashe biyu daga cikinsu,” in ji sanarwar.
Nwachukwu ya ce sun kuma kwato makamai da suka haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya, harsasai da kuma wani bindiga da aka kera cikin gida.
Sanarwar sojojin ta ce a shirye suke wajen tsaron rayuka da kuma dukiyoyin al’umma.
“Za mu ci gaba da ɗaukar matakai da suka dace kan ayyukan ƴan bindiga da suka addabi jama’ar yankin,” in ji sanarwar.