fidelitybank

Sojoji sun kashe ‘yan IPOB da suke nema ruwa a jallo

Date:

Rundunar soji ta kasa ta ce, ta kashe wasu ‘yan ƙungiyar IPOB biyu da take nema tare da lalata sansanin ƙungiyar a Jihar Imo da ke kudancin ƙasar.

Kakakin soji, Birgediya Janar Onyema Nwachuku, ya ce, dakarunsu tare da haɗin gwiwar ‘yan sandan DSS sun afka wa sansanin IPOB ranar Juma’a a Ƙaramar Hukumar Orlu.

“Dakaru sun lalata sansanin ba da horo bayan musayar wuta da su, inda aka kashe ƙasurguman miyagu biyu na ƙungiyar da ke cikin jerin mutanen da jami’an tsaro suka fi nema waɗanda suka addabi mazauna yankunan Orlu, da Orsu, da Njaba,” in ji sanarwar.

“Haka nan dakaru sun lalata wani wurin bauta da ‘yan ƙungiyar ke amfani da shi wajen yin addu’o’i, da kuma wani wurin haɗa makamai.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, sojoji sun ƙwace bindigar harba-ruga uku da ƙaramar bindiga ƙirar gida da kuma layu da sauran makamai.

punch news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp