Jami’an tsaro sun kashe ‘yan fashin daji shida a Ƙaramar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.
Wata sanarwa daga hedikwatar tsaron Najeriya da ke Abuja ta ce dakarun rundunar Operation Forest Sanity ne suka halaka ‘yan bindigar tare da haɗin gwiwar dakaru na musamman lokacin da suka kai samame kan maɓoyarsu a Maidaro.
Ta ƙara da cewa sojoji sun ƙwace makamai da harsasai masu yawa, sannan suka ƙona sansanin nasu.
“Yayin fafatawar, dakaru sun kashe ‘yan ta’adda shida kuma suka ƙwace bindigar AK-47 biyar, da ƙunshin harsashi 192,” a cewar sanarwar.