Dakarun sojin Najeriya, sun ceto wasu mutum tara da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.
Kazalika, dakarun rundunar Hadarin Daji, sun kashe ‘yan fashin daji 10 a harin da ta kai a safiyar yau Talata.
Wata sanarwa daga rundunar ta ce dakaru sun samu bayanan sirri ne na ƴan bindigar da ke shirin sace wasu daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su daga jihar Sokoto zuwa ƙauyen Gadazaima na jihar Zamfara.
Sojojin sun yi kwanton-ɓauna a cikin ƙauyen, inda aka yi musayar wuta tsakanin sojojin da ƴan bindigar na tsawon sa’o’i.
“Ƴan bindiga 10 ne aka kashe, yayin da wasu da dama suka tsere bayan an jikkata su,” a cewar sanarwar.
“Da yawan ƴan bindigar sun nitse cikin wani kogi da ke kusa da ƙauyen a yayin da suke ƙoƙarin tserewa. An yi nasarar kama biyu da kuma makamai masu yawa, da ƙudi naira miliyan 2,410,000, da kuma keken ɗinki.”