Shelkwatar tsaro ta kasa ta ce, sojojinta sun kashe mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da Islamic State West Africa Province (ISWAP) 120, cikin mako uku a Arewa maso Gabashin ƙasar.
Manjo Janar Bernard Onyeuko, shugaban sashen hulɗa da jama’a na rundunar, shi ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron manema labarai ranar Alhamis.
Ya ce, daga 20 ga watan Janairu zuwa Alhamis ɗin, dakarunsu sun yi nasarar kashe wasu kwamandojin ƙungiyar masu iƙirarin jihadin da kuma wasu mayaƙa ‘yan ƙasashen waje da ke haɗa musu ababen fashewa.
Ya ƙara da cewa mayaƙa 965 da iyalansu sun miƙa wuya ga sojoji a wurare daban-daban na Najeriya.
Adadin 104 na mutanen da ta kira ‘yan ta’adda na ƙungiyar ISWAP ne, yayin da aka ceto mutum 25 daga hannun ‘yan bindigar, in ji Mista Onyeuko.