Sojoji da ke aiki ƙarƙashin rundunar Operation Haɗin Kai a yankin arewa maso gabashin ƙsar sun halaka mayaƙan Boko Haram 17 yayin samamen da suka kai a sassan yankunan jihohin Borno da Adamawa.
Muƙaddashin Darakta a sashen hulɗa da jama’a na rundunar, Kyaptin Reuben Kovangiya, cikin wata sanarwa ya ce mayaƙan sun jima suna cin karensu babu babbaka a ƙananan hukumomin Bama da Konduga da Gwoza da Magumeri da Biu duka a jihar Borno da kuma Michika a jihar Adamawa.
Daily Trust ta ruwaito jami’in na cewa sojojin sun kuma gano tare da kwance fiye da abubuwan fashewa 14 da ƴan Boko Haram ɗin suka dasa a wurare da dama.
A cewarsa, abubuwan fashewar da aka dasa domin illata farar hula da sojoji, an yi nasarar kwance su a yayin samamen na jami’an soji.
Kovangiya ya ƙara da cewa a tsukin lokacin, sojoji sun samu damar maido da fiye da ƴangudunhijira 987 zuwa yankunansu a Mandaragau da ke ƙaramar hukumar Biu.
Ya ƙara da cewa matakin ya yi daidai da ƙudirin gwamnatin jihar Borno na sake tsugunar da mutanen yankin da kuma dawo da harkokin kasuwanci,” in ji shi.