Rundunar sojin kasar nan ta ce sojojinta tare da haɗin gwiwar ‘yan banga, sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga tare da kuɓutar da mata da kananan yara da aka sace a kauyuka daban-daban na jihar Borno.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar da shafin ta na X.
Rundunar ta kuma ce, sojojin sun kuma yi nasarar ƙwato makamai da sauran kayayyakin aiki iri-iri na ƴan bindigar.
Sojojin sun aiwatar da wani harin kwantan ɓauna a wuraren da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da mutane a kusa da Pulka da Ashagashiya dake ƙaramar hukumar Gwoza.
Sanarwar ta ƙara da cewa, a yayin samamen sojojin sun yi nasarar kashe ɗan bindiga ɗaya, yayin da wasu suka gudu cikin mawuyacin hali wanda suka bar kayansu.
Hakazalika sojojin sun kai wani harin kwantan bauna a yankin Komala na jihar Borno inda suka yi nasarar kashe wani ɗan bindiga tare da ƙwato makamai da alburusai.
A wani samame na dabam kuma a jihar Benue, sojojin da ke mayar da martani ga bayannan sirri kan ƴan bindiga a ƙauyen Ayati da ke karamar hukumar Ukum, sun ƙaddamar da wani samame cikin gaggawa domin dakile munanan ayyukan ‘yan bindigar.