Sojojin Najeriya daga runduna ta shida sun kashe ƴanbindiga biyu a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Bali da ke jihar Taraba.
Rundunar ta ce sojojinta ne suka kai samamen bayan samun bayanan sirri game da kasancewar ƙungiyoyin ƴanbindiga a yankunan Nayinaya da Garin Daniel da Garbatau.
A cewar rundunar, sojojin sun yi fito na fito da ƙungiyoyin ƴanbindigar inda suka yi nasarar kashe biyu daga cikin su tare fa ƙwato muggan makamai – bindigogi da kuma alburusai.
Rundunar ta ce tana ci gaba da gudanar da aiki tuƙuru domin fatattakar ƴanbindiga da masu aikata miyagun laifuka a jihar har sai an samar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Kwamandan runduna ta shidan ya yaba wa sojojin bisa ƙoƙarin da suka yi inda kuma ya yi kira ga jama’a da su samar da bayanai a-kai-a-kai da za su kai ga murƙushe miyagu.