fidelitybank

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga a Katsina da Kaduna

Date:

Dakarun sojojin kasa sun kashe wasu ‘yanbindiga huɗu a wani samame da suka kai jihohin Kaduna da Katsina.

Sanarwar da Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce, sojojin sun kuma dakile yunkurin yin garkuwa da shugaban makarantar firamare a jihar Filato.

Sanarwar ta ce, bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa ana amfani da hanyar Gwamtu – Duduwa-Kujeni da ke karamar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, wajen kai wa ƴan bindiga kayaki a dajin Rijana, sai sojoji suka yi wa wajen kwanton bauna, inda suka hallaka biyu daga cikin ƴan bindigar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, a wani samame da sojoji suka yi nasarar kai wa a maɓoyar ‘yan bindiga da ke Dutsen Kura a karamar hukumar Batsari na jihar Katsina, sun yi nasarar kashe guda biyu, bayan musayar wuta da su. In ji BBC.

Sanarwar ta kuma ce, a samame da aka kai jihar Filato, sojojin sun dakile yunkurin yin garkuwa da wani Mista Solomon Zakka, shugaban makarantar Pilot Primary School, Daffo, wanda aka so yin garkuwa da shi a gidansa da ke kauyen Maiduna a karamar hukumar Bokkos.

naija news today legits

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp