fidelitybank

Sojoji sun kashe shugaban ‘yan fashin dajin Sokoto

Date:

Rundunar Sojin kasa ta kashe wani jagoran ‘yan fashin daji a jihar Sokoto.

Wata sanarwa da ta fitar a shafukanta na intanet ta ce dakarun rundunar da aka tura don yaƙi da ta’addanci ne suka yi nasarar kashe jagoran, wanda ba ta bayyana sunansa ba, a ranar Laraba.

“Bayan samun bayanan sirri, dakaru sun yi wa gungun ‘yanta’addan kwanton-ɓauna a wata mashiga da ke ƙauyen Sarma a ƙaramar hukumar Tangaza, inda suka yi nasarar kashe jagoransu tare da ƙwato bindigar AK-47 da kuma babur,” in ji sanarwar.

A jihar Kaduna kuma, dakarun sojin sun yi nasarar katse hanzarin masu garkuwa da mutane a garin Kafanchan na ƙaramar hukumar Jema’a, sannan suka kama biyu daga cikinsu tare da ƙwato bindiga ɗaya, da harsasai, da kuma babur.

Kazalika, wani ɗan fashi ya gamu da ajalinsa a wurin duba ababen hawa na Kaskara da ke ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato, lokacin da dakarun suka amsa kiran neman agaji game da gungun ‘yanfashi a yankin.

world news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp