Dakarun tsaron sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wani rikakken ɗan bindiga da aka fi sani da suna Mai-Nasara a dajin Sangeko na jihar Kebbi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito wata sanarwa da Alhaji Ahmed Idris, babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Kebbi ya fitar na cewa jami’an tsaron sun kama mutum biyar da ake zargin ‘yan fashin daji da ke cikin gungun masu aikata laifuka.
Ya ambato gwamnatin Kebbi ta yaba da jajircewar jami’an tsaron wajen yaƙi da miyagun laifuka musamman a yankin kudancin jihar.
“Goyon bayan jama’a da hadin kanku ya zama wajibi sosai domin jami’an tsaro su cimma burin da ake so na fatattakar masu aikata laifuka da kuma dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu.”
Ya ja hankalin jama’ar yankin su yi kokarin taimakawa jami’an tsaro ta kowanne fanni, musamman da sahihan bayanan sirri don samun nasarar fada.”