Dakarun Operation FANSAR YANMA sun yi nasarar fatattakar wani kasurgumin dan fashi da makami mai suna Dan Dari Biyar a wani samame da suka kai a unguwar Sabon Birni dake jihar Sokoto.
Majiyoyin soji sun tabbatar da cewa an kashe shugaban ‘yan fashin ne a ranar Alhamis yayin da yake yunkurin karbar kudin fansa daga ‘yan uwan wadanda aka yi garkuwa da su a cikin dajin da ke tsakanin kauyukan Turtsawa, Mazau, da Zango.
An bayyana hakan ne a wani sako da wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ya fitar a ranar Asabar ta hanyar X:
“Sojoji sun kashe fitaccen dan ta’addan Dan Dari Biyar a Sabon Birni, jihar Sokoto a lokacin da yake kokarin karbar kudin fansa, ya jagoranci kai hare-hare a wasu al’ummomi da dama.
Rahotanni sun bayyana cewa Dan Dari Biyar ya shahara da zaluntarsa, inda ya rika yin izgili da wadanda abin ya shafa kafin a biya su makudan kudade. An ce yana can ne a cikin dajin Tidibale, kuma yana kai hare-hare a Lalle, Tsamaye, Gidan Sale, da wasu sassan Gwadabawa da Gwaronyo.
Bayanan sirri na sojoji sun alakanta shi da wasu hare-hare na kwanton bauna, samame da kone-kone a shiyyar Sanatan Sakkwato ta Gabas.
Wannan farmakin da sojojin suka gudanar tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na cikin gida a karkashin shirin gwamnatin jihar Sokoto na kare al’umma, ya kuma kai ga kwato makamai, alburusai, da na’urorin sadarwa.