fidelitybank

Sojoji sun kashe riƙaƙen ɗan bindiga Guddel a Kaduna

Date:

Sojoji sun yi nasarar kawar da fitaccen shugaban ‘yan bindiga Guddel da dan uwansa a wani samame da sojoji suka yi a jihar Kaduna.

An bayyana hakan ne a wani sako da wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Bakatsine ya wallafa a shafin X.

An ce Guddel shi ne ke da alhakin kai hare-hare da sace-sacen mutane da dama a sassan Kaduna da jihohin da ke makwabtaka da ita.

Bakatsine ya rubuta cewa: “Sojoji sun yi nasarar kawar da dan bindiga Guddel da dan uwansa a Kaduna.

A wani labarin makamancin haka, Bakatsine ya kuma ruwaito cewa rikicin da ya barke tsakanin ‘yan bindiga a garin Danmusa na jihar Katsina ya kai ga tserewa wasu da aka yi garkuwa da su daga Kankara.

Ya kara da cewa, “Rikicin da aka yi tsakanin ‘yan bindigar Danmusa ya taimaka wa wadanda aka yi garkuwa da su daga Kankara su tsere, an kashe ‘yan bindiga da dama, ciki har da wani babban shugaba a rikicin,” in ji shi.

Har ya zuwa lokacin wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da lamarin ba.

guardian newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp