Rundunar sojoji ta kasa ta ce, sojoji da ke yaki da kungiyoyin Boko Haram/ ISWAP sun kashe mayakan kungiyoyin da dama, ciki har da shugaban addini na Galta, a wani samame da ta kai musu.
Sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na Tiwitter ta ce, samamen ya auku ne a yankin Manjo Ali Qere da ke jihar Borno.
Sanarwar ta kuma ce, harin ya auku ne ranar Alhamis 28 ga watan Afrilun 2022, kuma ta ce an kama makamai da harsasai.