Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla mayaƙan Boko Haram/ISWAP takwas a wani artabu da ya ɓarke a ƙauyen Manawaji, cikin ƙaramar hukumar Gamboru Ngala da ke jihar Borno.
Rundunar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Litinin, 30 ga Yuni, 2025.
Rundunar sojin Operation Hadin Kai, tare da hadin gwiwar ƙungiyoyin ƴan sintiri na CJTF da dakarun Hybrid Forces ne sun gudanar da wannan nasarar.
A yayin gumurzu mai zafi da suka fafata da mayaƙan, dakarun sun samu nasarar kashe guda takwas daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da raunuka.
“Bayan kammala fafatawar, sojojimu sun ƙwato bindigogi da dama da harsasai daga hannun mayaƙan da suka mutu da kuma waɗanda suka tsere.” In ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa “Babu wanda ya jikkata ko ya mutu daga ɓangaren sojoji, da sauran da aka yi haɗin gwiwa da su.”
Hukumomin tsaro sun bayyana cewa an ƙara matsa ƙaimi wajen sintiri da tabbatar da tsaro a yankin Gamboru Ngala da kewaye, domin hana mayar da su mafakar ƴan bindiga.
A halin yanzu, an ce yankin ya dawo daidai, sai dai har yanzu ana cigaba da lura da al’amura domin gudun duk wata barazana.