fidelitybank

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Date:

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla mayaƙan Boko Haram/ISWAP takwas a wani artabu da ya ɓarke a ƙauyen Manawaji, cikin ƙaramar hukumar Gamboru Ngala da ke jihar Borno.

Rundunar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Litinin, 30 ga Yuni, 2025.

Rundunar sojin Operation Hadin Kai, tare da hadin gwiwar ƙungiyoyin ƴan sintiri na CJTF da dakarun Hybrid Forces ne sun gudanar da wannan nasarar.

A yayin gumurzu mai zafi da suka fafata da mayaƙan, dakarun sun samu nasarar kashe guda takwas daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da raunuka.

“Bayan kammala fafatawar, sojojimu sun ƙwato bindigogi da dama da harsasai daga hannun mayaƙan da suka mutu da kuma waɗanda suka tsere.” In ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Babu wanda ya jikkata ko ya mutu daga ɓangaren sojoji, da sauran da aka yi haɗin gwiwa da su.”

Hukumomin tsaro sun bayyana cewa an ƙara matsa ƙaimi wajen sintiri da tabbatar da tsaro a yankin Gamboru Ngala da kewaye, domin hana mayar da su mafakar ƴan bindiga.

A halin yanzu, an ce yankin ya dawo daidai, sai dai har yanzu ana cigaba da lura da al’amura domin gudun duk wata barazana.

tribune

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

INEC za ta fitar da sabbin ƙa’idojin duba sakamakon zaɓe

A shirye-shiryen da take yi gabanin babban zaɓen Najeriya...

Isra’ila ta amince da sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Isra'ila ta amince...

Buhari ba zai taɓa cin amanar Tinubu ba – Garba Shehu

Tsohon babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai...

Mutane 207 ne suka mutu a ambaliyar Neja – NSEMA

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta...

Jiga-jigan jam’iyyar PDP za su sauya sheƙa don tunkarar APC a 2027

Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP da suka hada da tsohon...

Za a ƙaddamar da jam’iyyar hammaya da za ta tunkari APC

Gamayyar jam'iyyun adawa a ranar Talata, ta amince da...

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla...

Sauya sunan Kwaleji a Oyo ya fusata Dalibai

Ɗaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga...

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta'aziyya...

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...
X whatsapp