fidelitybank

Sojoji sun kashe manyan kwamandojin Boko Haram a Borno

Date:

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce, sojojinta masu aiki ƙarƙashin shirin ‘Operation Hadin Kai’ da ke yaƙi da ayyukan masu tayar da ƙayar baya sun kashe manyan kwamandojin Boko Haram a hare-hare ta sama da suka kai a a ranar 16 ga wannan wata na Agusta a jihar Borno.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta AVM Edward Gabkwet a yau Laraba.

Sanarwar ta ce “rundunar ta kai harin ne kan ƴan ta’addan da suka yi hijira zuwa yankin daga wasu wurare da ke kusa”.

“Hare-haren sojojin ta sama sun yi nasarar halaka ƴan ta’adda da dama da suka hada da manyan kwamandojinsu biyar da kuma yaransu 35 tare da lalata maɓoyarsu da kayan aikinsu.

“Bayanai masu ƙarfi da aka tattara sun nuna cewa manyan ƴan ta’adda da ke a wurin da aka kai harin a daidai lokacin sun haɗa da Munzir Arika, Sani Dilla (Dan Hausawan Jubillaram), Ameer Modu, Dan Fulani Fari Fari, da Bakoura Arina Chiki, sai kuma sauran wasu ƴan bindiga 35.”

Sanarwar ta ce “Ana sa ran nasarar kashe waɗannan kwamandojin da mayakansu zai rage ƙarfin wadannan kungiyoyi ƴan ta’adda na ƙara kai hare-hare ko sake haɗuwa a yankin.”

Najeriya na yaƙi da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram tsawon sama da shekaru 10 da suka gabata, rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban al’umma da kuma tarwatsa sama da mutum miliyan ɗaya daga gidajensu.

Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta yi iƙirarin karya lagon mayaƙan, amma har yanzu akan samu hare-hare nan da can a yankin na arewa maso gabashin ƙasar.

A ƙarshen watan Yuli, wasu mayaƙa da ake zargin ƴan Boko Haram ne sun kai hari a jihar ta Borno wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 16.

vanguard new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp