Sojojin Najeriya sun, ce sun kashe ɗaya cikin manyan kwamandojin Iswap da wasu mayaƙa a wani farmaki a arewa maso gabashi.
Sojojin sun ce sun kashe kwamandan mai suna Abubakar Danbuduma da mayaƙa 19.
Rundunar sojin ta ce dakarunta sun kai harin ne a yankin Tafkin Chadi ta hanyar amfani da jiragen yaƙi.
Abu ne mai wahala a iya tantance gaskiyar labarin. Amma wannan na zuwa a yayin da mayaƙan Iswap ke karɓe ikon wasu ƙauyuka tana tilasta wa mutane biyan haraji