Dakarun rundunar sojin Operation Hadin Kai’ dake Arewa maso Gabas, sun yi nasarar kawar da wani babban kwamandan kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, wanda aka fi sani da Boko Haram, Tahir Baga.
Hakan ya biyo bayan ci gaba da kai gaggarumin farmakin da sojojin suka kai a dajin Sambisa.
Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, majiyoyi sun bayyana cewa an kashe Tahir ne a ranar 13 ga Mayu, 2024, lokacin da sojojin da suka kaddamar da wani gagarumin farmaki mai suna ‘Operation Desert Sanity III’, sun yi nasarar fatattakar ‘yan kungiyar Shababul Umma, a Garin Panel Beater da Lagara Anguwan Gwaigwai.
Majiyoyin Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, su ma sun tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Talata.
Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Tahir Baga
Date: