Sojoji sun ce, sun kashe wani jagoran ƴan fashin daji a jihar Kaduna mai suna Dogo Maikasuwa.
Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya fitar ranar Juma’a ta ce an halaka Maikasuwa ne lokacin da dakarun suke sintiri a Ƙaramar Hukumar Chikun.
Sanarwar ta ce jami’an tsaron sun samu nasarar ƙwato bindiga ɗaya ƙirar AK-47, da alburusai, da babura biyu da kuma kakin soja.
Ta ƙara da cewa Dogo Maikasuwa, wanda ake kira da Maimilliyan, ya jagoranci kai hare-hare da garkuwa da mutane masu bin hanyar Kaduna zuwa Kachia da kuma wasu kauyuka na Chikun.


