Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta samu nasara halaka wasu ‘yan bingida a jihar Naija ciki har da wani gawurtaccen ɗan bindiga da ya jima yana addabar jama’a, mai suna Yellow Jambros.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fita mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaranta, Air Commodore Edward Gabkwet, ta ce ‘yan bindigar sun gamu da ajalisun ne a ranar Laraba 6 ga watan Disamba a gundumar Galadima Kogo, a daidai lokacin da suke yunƙurin tsallaka kogi zuwa yankin Wurukuvhi na ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna mai makwabtaka.
Kafin kisan nasu, an yi ta bin diddigin Yellow Jambros, tare da mabiyansa waɗanda suka taso daga jihar Zamfara a kan babura 13 inda suka nufi Kusasu na ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Naija.
Sanarwar ta ce da suka isa Kusasu, wasu ƙarin babura biyar sun shiga tawagar tasu, inda suka zama babura 18, daga nan kuma suka nufi kogin Jikudna.
”Da isarsu kogin ne ‘yan bindigar suka hau kwale-kale tare da baburansu 18 da nufin tsallakawa, suna tsaka da kogin ne kuma aka bayar da umarnin kai musu hari”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Air Commodore Edward Gabkwet ya ce an samu nasarar ƙaddamar da harin yadda aka tsara shi, inda aka kashe Yellow Jambros da sauran yaransa tare da lalata baburan da kuma nutsar da kwale-kwalen.
”Duk da cewa tafiyar ‘yan bindiga cikin ayari ba abu ne da aka saba gani ba, musamman da rana tsaka, Yellow Jambros tare da yaransa ba su yi tsammanin kai musu hari ta sama ba, saboda suna tunanin sojoji sun dakatar da kai hare-hare ta sama saboda da abin da ya faru na harin kuskure kan fararen hula a Tudun Biri, don haka suke son yin amfani da wannan damar”, in ji Edward Gabkwet.
Ya ƙara da cewa Yellow Jambros tare da yaransa sun sha ƙaddamar da hare-hare tare da yin garkuwa da mutane da kuma kashe su a kan babban titin Abuja zuwa Kaduna da kuma wasu garuruwa a jihohin Kaduna da Naija da Katsina da kuma Zamfara.
A watan Oktoban 2020 ‘yan sandan Zamfara suka kama wani gawurtaccen ɗan bindiga mai suna Mohammed Sani, wanda ya kashe fiye da mutum 50, saboda sun kasa haɗa masa kuɗin fansar da ya buƙata daga gare su.
A lokacin da ‘yan sandan ke tuhumarsa ya yi iƙirarin cewa shi yaron Yellow Jambros ne, wanda ke samar masa da jabun tufafin sojoji da na ‘yan sanda da bindigogi da sauran makaman da yake buƙata. In ji BBC.