Gwamnatin jihar Kaduna ta ce, jami’an tsaron haÉ—in gwiwa sun kashe wani jagoran ‘yanfashin daji mai suna Alhaji Kachalla Ragas tare da wasu abokan harkallarsa da dama.
Wata sanarwa da Kwamashinan Tsaro Samuel Aruwan ya fitar a yau Juma’a, ta ce dakarun rundunar Operation Whirl Punch ne suka yi nasarar kashe shi bayan hare-haren da suka kai ta sama a Æ™aramar hukumar Giwa da ke jihar.
Sanarwar ta kuma ce, hare-haren dai ta sama da ta Æ™asa sun yi nasarar kashe ‘yanbindiga da yawa tare da shugabanninsu a dajin Yadi da ke yankin Bula.
Ya Æ™ara da cewa an kai harin ne bayan samun bayanan sirri cewa ‘yanbindigar za su yi wani taro domin kitsa mummunan aiki, daga baya masu leÆ™en asiri suka hangi gungun mutane bakwai zuwa 10 É—auke da makamai.
Aruwan ya ce, cikin waÉ—anda aka kashe har da Alhaji Kachalla Ragas, wanda abokin Buharin Yadi ne wanda shi ma aka kashe kwanan nan.