Rundunar sojojin Ć™asa ta ce, dakarunta sun kashe wasu ‘yan kungiyar IPOB biyu da ke neman ballewa daga Najeriya a wani ba-ta-kashi da suka yi.
A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Talata, ta ce, dakarun na ta sun kuma kama ‘ya’yan kungiyar ta IPOB guda hudu a Orlu da ke jihar Imo a kudu maso gabashin kasar ranar 25 ga watan Afrilun 2022.
Sanarwar ta kara da cewa, binciken da aka gudanar a wayoyin salula na mutanen ya nuna hotuna da bidiyo na mutanen da aka kashe a wuraren bauta na gargajiya.
Kazalika an gano bindigogi da sauran miyagun abubuwa a hannun mutanen, in ji rundunar sojin