Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji daga arewa maso yamma, sun kashe ‘yan ta’adda hudu a jihar Zamfara.
An kashe su ne a lokacin da sojoji suka kai wa ‘yan fashin hari a wasu sansanoni da aka gano a kauyukan Tazame, Mashema, Gandaya, Maje, Doka da kuma yankunan da ke makwabtaka da kauyen Gandaya a karamar hukumar Bungudu ta jihar.
Sanarwar da hukumomin sojin suka fitar ta ce wasu ‘yan bindigar da ba a tabbatar da adadinsu ba sun tsere da yiwuwar harbin bindiga.
Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa an kwato shanu hamsin da bakwai, da kakin soji, da kayan barci da kuma Naira dubu dari tara (tsabar kudi) daga maboyar ‘yan ta’addar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Dukkan ‘yan ta’addan da aka gano da kuma sansanonin wucin gadi an lalata su nan take a yayin farmakin”.
Wannan na zuwa ne sa’o’i ashirin da hudu bayan da sojojin suka kubutar da mutane 31 da aka yi garkuwa da su daga majiyar ‘yan bindiga a Sokoto, sannan kuma an lalata sansanoni da dama.