fidelitybank

Sojoji sun kashe ɗan fashin dajin Bauchi

Date:

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kashe dan fashi guda a wani ƙwanton-ɓauna da sojojin suka yi wa tawagar ‘yan fashin a yankin Bura na ƙaramar hukumar Ningi da ke jihar Bauchi.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Asabar, mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Burgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce sojojin sun amfani da bayanan sirri da suka samu game da ‘yan fashin.

“Sojojin sun yi wa ‘yan fashin kwanton-ɓauna tare da buɗe musu wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar guda daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbin bingiga a jikinsu”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sojojin sun kuma ce sun samu nasarar ƙwato bindiga guda ƙirar Ak-47 da alburusai 14, da wayar hannu da kuma guru da layu daga ɗan fashin da suka kashe.

Sanarwar ta kuma ce sojojin na ci gaba da sintiri a yankin domin gano sauran ‘yan fashin da suka tsere.

Yankin arewa maso yammacin Najeriya ne dai ya fi fama da matsalar ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane, to sai dai a baya-bayan matsalar ta fara ɓulla a wasu yankunan jihar Bauchi da ke kudu maso gabashin ƙasar.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp