fidelitybank

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Date:

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar Chana, bisa zarginsa da hannu wajen kai wa ’yan ta’adda kayayyaki a jihar Borno.

Daraktan Yada Labaran Shalkwatar Tsaron Ƙasar nan Manjo Janar Markus Kangye ne, ya bayyana hakan ranar Juma’a a Abuja, yayin ganawa da manema labarai.

Ya ce, an kama mutumin ne a wani samame da sojoji suka gudanar a kananan hukumomin Kukawa da Ngala da ke jihar Borno, inda ake zargin yana fakewa da aikin hakar ma’adanai.

Kangye ya ce yanzu haka an tsare dan Chanan, kuma ana masa tambayoyi domin gano hakikanin abinda ya kai shi yankin da kuma yiwuwar ko akwai wasu da ke tare da shi.

Ya kara da cewa bayan kammala bincike, za a bayyana wa jama’a cikakken bayani kan abin da ya faru, da matsayin da wanda ake zargin ke ciki.

Sojojin sun kuma sanar da cewa daruruwan ’yan Boko Haram da ISWAP sun mika wuya daga ranar 6 zuwa 11 ga Yuni, sakamakon yadda suka tsananta ayyukan tsaro a yankin arewa maso gabas.

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansani a Kebbi

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta...

Za afara rijistar masu zabe a Najeriya – INEC

Hukumar zaɓe ta INEC, ta ce, nan gaba cikin...

Ma’aikatan Jinya sun dakatar da yajin aiki a Najeriya

Ministan lafiya a Najeriya ya ce, ma'aikatan jinya da...

Izak ya na ɗaukar horo bayan ya dage sai ya koma Liverpool

Ɗanwasan gab ana Newcastle Alexander Isak na can yana...

Masu tsaigunta wa ƴan Bindiga ne ke haddasa kashe-kashe – Gwamnan Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ce masu tsegunta wa ƴanbindiga...

Gwamnoni ku yi wa mutanen ƙauyika da karkara ayyuka – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci gwamnonin ƙasar nan su...

Dino Melaye ya gudu daga PDP ya faɗa ADC

Tsohon ɗan jamalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma,...

Isra’ila na zargin Canada da goyon bayan Hamas – Netanyahu

Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan...

Rashin tallafin agaji ka iya dawo da Boko Haram a Najeriya – MDD

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta...

Yin gini a kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta...

Amnesty ta yi Allah wadai da tsare Sultan kan bidiyon lafiyar Tinubu

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi...

Dalilin da ya sa na gana da Tinubu – Kofa

Ɗan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga...
X whatsapp