fidelitybank

Sojoji sun kama shugaban PDP na mazaba a Zamfara da tallafawa ‘yan bindiga

Date:

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin (OPHD) sun kama wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a jihar Zamfara.

Daya daga cikin wadanda ake zargin, Aminu Ibrahim, ana zarginsa da kasancewa shugaban jam’iyyar PDP, shugaban gundumar Birnin Yero a karamar hukumar Shinkafi a jihar.

Wata majiyar leken asiri ta soji a jihar ta ce an kama Ibrahim, tare da abokan sa da aka fi sani da Musa Usman Seun da Isah Mohammed ranar Litinin.

Majiyar ta ci gaba da cewa: “Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Haderin Daji sun yi aiki da sahihan bayanan sirri kan ayyukan wani dan bindiga da ya yi yunkurin shigo da makamai cikin jihar.

Wannan kafar yada labarai ta kuma samu labarin cewa sojojin sun yi gaggawar tare hanya inda suka kame mutanen uku da ake zargin ‘yan bindiga ne.

“Wadanda ake zargin su 3, Musa Usman Seun, Aminu Ibrahim, da Isah Mohammed, an kama su ne a Shinkafi a ranar 22 ga watan Janairun 2024, kuma an kama su da kudi naira miliyan biyu da dubu dari biyar da tamanin, Volkswagen Wagon 1, wayoyin hannu 3 da sauran kayayyaki.

“Bincike na farko ya nuna cewa makudan kudaden da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin na musayar muggan makamai ne a kan iyakar Illela a jihar Sakkwato. Ana ci gaba da yi wa wadanda ake zargin tambayoyi.”

naija news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp