Rundunar soji ta musamman ta Operation Safe Haven (OPSH) da ke wanzar da zaman lafiya a Filato da wasu sassan jihohin Kaduna da Bauchi ta kama wasu mutane 13 da ake zargi da laifin satar mutane, fasa gidan yari, fashi da makami, sata da sauran laifuka.
Jamiāin yada labarai na kungiyar OPSH, Kyaftin James Oya a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Jos, ya ce sojojin sun kuma kwato shanu 279 da aka sace da makamai da alburusai.
Oya ya bayyana cewa, OPSH ta samu nasarar ne a wani samame da ta gudanar tsakanin ranakun 2 zuwa 9 ga watan Oktoba, inda ta kara da cewa an kama wadanda ake zargin ne a wasu alāummomi da ke yankunan da ke karkashinta.
āāTsakanin ranar 2 ga watan Oktoba zuwa 9 ga watan Oktoba, sojojin mu sun kama wasu mutane 13 da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi garkuwa da mutane, fasa gidan yari, safarar miyagun kwayoyi da kuma sata.
”Mun kuma kwato haramtattun makamai da alburusai.
āāSojoji sun kwato shanu 279 da tumaki shida bisa lalata amfanin gona a filayen noma a fadin kananan hukumomin Bokkos, Mangu, Riyom da Zango Kataf (LGAs) na jihohin Filato da Kaduna, bi da bi.ā Inji Oya.