Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta tare da hadin gwiwar ‘yan banga sun cafke wani da ake zargin dan bindiga ne a Taraba.
Wanda ake zargin, Mansir Mohammed, an kama shi ne a tashar mota ta Jalingo bisa zarginsa da bayar da makamai ga ‘yan ta’adda.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Maj.-Gen. Onyema Nwachukwu, ranar Litinin a Abuja.
Nwachukwu ya ce sojojin sun kuma dakile yunkurin yin garkuwa da su tare da kawar da wani dan ta’adda a yayin samamen.
Ya ce kama Mohammed ya kai ga kama wasu mambobin kungiyarsa tare da kwato bindigar Semi-Automatic Pump Action guda daya.
Ya ce sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da bindiga guda daya, mota kirar Peugeot, wayoyin hannu guda biyar, da kudi N45,000.
Nwachukwu ya ce sojojin sun yi wani samame na daban a kauyen Miyande da ke karamar hukumar Takum a jihar, sun kama wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne guda biyu da suka boye bindigogi masu sarrafa kansu a karkashin kujerar babur.
Ya kara da cewa an kwato bindiga kirar AK- 47 guda 5, harsashi na musamman mai girman 7.62mm da kuma babur a hannun su.
“A wani labarin kuma, sojojin sun amsa kiran da aka yi musu na nuna bacin rai, inda suka yi nasarar dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a garin Zaki-Biam da ke karamar hukumar Zaki-Biam a jihar Benue.
“A yayin shiga tsakani, sojoji sun kashe wani mai garkuwa da mutane a wata musayar wuta da masu laifin tare da kwato bindigar Beretta tare da harsashi hudu na tara.
“Wadannan ayyuka da suka samu nasara suna nuna jajircewar rundunar sojin Najeriya wajen kawar da ta’addanci da tada kayar baya a yunkurinta na tabbatar da tsaro a kasar.
“Muna kira ga jama’a da su ci gaba da ba sojojinmu goyon baya yayin da suke gudanar da ayyukansu,” in ji shi.