Rundunar hadin gwiwa ta Operation Delta Safe (OPDS), ta kama wani jirgin ruwa tare da ma’aikatansa biyu a jihar Ribas, ɗauke da lita 300,000 na gas da aka tace ba bisa ƙa’ida ba.
An kama jirgin ne a tashar jirgin ruwa da ke Onne, a jihar Ribas cikin kogin Bonny.
Commodore John Siyanbade, wanda ke wakiltar kwamandan OPDS, Olusegun Ferreira ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Fatakwal.
An kama jirgin ruwan ne a ranar 29 ga Oktoba, 2023.
Jirgin yana jigilar gas ne ba bisa ƙa’ida ba, kuma ana amfani da shi a zaman wurin ajiyar wannan haramtaccen kayan.
An tsare mutane biyu da ake zargi da ke cikin jirgin kuma za a miƙa su ga hukumomin da suka dace domin gurfanar da su a gaban kuliya.
Kwamanda Siyanbade ya kuma yi gargaɗi ga duk masu hannu a irin wannan ayyukan da su daina ayyukansu cikin gaggawa domin gujewa fuskantar shari’a.