Rundunar sojin ruwan kasar nan, ta ce, ta kama wasu mutane dauke danyen man fetur lita 3,500 a cikin wani jirgin ruwa na katako a kan hanyarsa na zuwa kasar Kamaru.
Kwamandan rundunar, Kaftin Uche Aneke, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mika wadanda ake zargi da kayayyakin ga hukumar tsaro ta Civil Defence a Ibaka dake jihar Akwa Ibom ranar Talata.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a kan hanyar ruwa da misalin karfe 11:15 na safiyar ranar 18 ga watan Mayu.
Ya ce, rundunar sojin ruwan ta samu rahoton da ake zargin ana fasa kwaurin ne a yankin da take aiki.
Da yake karbar wadanda ake zargin da kayayyakin, Michael Asibor, kuma shugaban sashin dake kula da barnata kayan gwamnati na hukumar tsaro ta civil defence, ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.