Rundunar sojin ruwa ta kasa, ta kama wani jirgin ruwa ɗauke da gangar mai 3,665 da take zargi na sata ne a yankin Igbokoda na jihar Ondo.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce ta kama ma’aikatan jirgin 17, da take zargi da satar man daga rijiyar mai ta Ebesan a ƙaramar hukumar Ilaje da ke jihar.
Daraktan yaɗa labaran rundunar, Commodore Ayo-Vaughan, ya ce an kama jirgin ne a ranar Alhamis.
Ya ce rundunar ta samu bayanan sirri kan ayyukan mutanen da take zargi da sace man, inda nan take ta tura jami’anta waɗanda suka yi nasarar kama mutanen.
Sanarwar ta ce sojojin sun gano cewa an daɗe ana amfani da jirgin wajen satar man daga kowane ɓangare na rijiyar.
Jirgin na da girman da zai iya ɗaukar nauyin metric ton 15,000, kuma a lokacin da aka kama shi yana ɗauke da man da nauyinsa ya kai metric ton 500.
Satar mai a kudancin Najeriya dai wata matsala ce da ta daɗe tana ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya, inda ɓata-gari ke sace ɗimbin mai ta hanyar fasa bututan man ko amfani da rijiyoyin mai ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ke ƙara haifar da koma-baya kan tattalin arzikin ƙasar.