Jami’an rundunar sojin ruwa ta ƙasar nan, sun gano wani gida mai zaman kansa da aka mayar da shi wurin tace haramtacciyar hanya a unguwar Okwuzi da ke karamar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni a jihar Ribas.
Kwamandan hukumar ta NNS Pathfinder, Commodore Desmond Igbo ne ya jagoranci tawagar sojojin a rangadin da suke aikin tace matatun ba bisa ka’ida ba, ya kuma shaidawa manema labarai a ranar Juma’a cewa an kwace sama da lita 200,000 na man fetur na Automotive Gas Oil, AGO, wanda aka fi sani da diesel.
An kama wasu mutane biyu da ake zargi yayin samamen.
Commodore Igbo ya bayyana cewa, an gano hakan ne bisa umarnin hafsan hafsoshin ruwa na yaki da satar danyen mai da kuma munanan ayyuka a yankin na Niger Delta, ta hanyar hadin gwiwa na leken asiri.
Kwamandan ya bayyana adadin kayayyakin da aka tace ba bisa ka’ida ba a wurin da yawa, inda ya ce an yi wa wasu buhuna, wasu an ajiye su a cikin ganguna, an kuma cika tankoki sama da 62.
Ya tabbatar da cewa an samu sama da lita 200,000 na haramtattun kayayyaki da aka tace daga danyen mai da aka tono ko aka sace daga bututun mai.
Commodore Igbo ya nunar da cewa za a mika wadanda ake zargin ga hukumomin shari’a kuma za a rufe harabar.
Ya kuma shawarci matasan yankin da kada su bari a yi amfani da su a matsayin kayan aikin zagon kasa ga tattalin arzikin kasa.