Rundunar sojin Najeriya ta ce, hadin gwiwar runduna ta 82, da ‘yan sandan Najeriya da jami’an tsaro sun yi nasarar kai samame a maboyar ‘yan kungiyar IPOB/ESN da ke dajin Orsomoghu, wadanda suka hada da jihohin Anambra da Imo.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an sanar da sojojin game da ta’addancin kungiyar IPOB/ESN a Onitsha, Nnewi da Iheme Obosi a jihar Anambra, da kuma sabuwar kasuwa a jihar Enugu.
A cewar sanarwar, a yayin gudanar da aikin, sojojin sun fatattaki ‘yan kungiyar ta IPOB da ke Ekeututu, Orsomoghu, Lilu da kuma Mother Valley na ‘yan tawayen.
Ya ce dakarun sun yi arangama da mayakan kungiyar da ke dauke da makamai, inda suka tayar da bama-bamai (IED) da aka fi sani da Ogbunigwe ta hanyar amfani da bututun turmi na cikin gida.
Sanarwar ta ce, “Jajirtattun sojojin sun yi galaba a kan ‘yan kungiyar da ba su ji ba gani a harin, inda suka tilasta musu barin matsayinsu yayin da suke gudu da raunukan harbin bindiga a cikin dazuzzuka,” in ji sanarwar.
Yace tr