Dakarun sojojin Najeriya da aka tura yankin Arewa maso Gabas a ci gaba da kai farmakin da ‘yan ta’addan ke ci gaba da yi a ranar Juma’a, sun yi nasarar kai wani samame a sansanin ‘yan ta’adda da ke yankin Arra a dajin Sambisa, inda suka yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga uku tare da lalata musu matsugunin su.
Major General Onyema Nwachukwu,
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce sojojin sun kwato bindigogin AK-47 guda biyu da rigar kunar bakin wake.
“A wani farmakin da sojojin suka kai a yankin Buluwa da ke karamar hukumar Kukawa a jihar Borno, inda suka gano tare da lalata wani sansanin ‘yan ta’addan,” in ji shi.
Ya ce yayin arangamar sojojin sun kashe dan ta’adda guda daya tare da kwato bindiga kirar AK-47 guda 14, 7.62mm (Special), keke, kayan abinci, injin nika, da sauran kayayyaki.
Ya ce rundunar sojin Najeriya ta dukufa wajen ganin ta kawar da ta’addanci da tada kayar baya a yankin, kuma za ta ci gaba da gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro da tsaron jama’a.S


 

 
 