Rundunar sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar rundunonin sojojin hadin gwiwa da na Civilian Joint Task Force, sun yi nasarar kai farmaki a yankin tafkin Chadi da kungiyar Boko Haram/Islamic State West Africa Province, ISWAP.
A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Maj.-Gen. Onyema Nwachukwu, a ranar Juma’a a Abuja, an gudanar da wannan farmakin ne a ranar Larabar da ta gabata tare da gwabza kazamin fada, inda aka kashe ‘yan ta’adda uku tare da kwato wata mota kirar Mine Resistant Ambush Protected, MRAP.
Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da wata babbar mota makare da bindigar kakkabo jirgin da tarin makamai da harsasai.
A cewar Nwachukwu, ‘yan ta’addan sun far wa sojojin ne da wata mota kirar Bama-bamai, VBIED, turmi, manyan bindigogi da kuma babura.
Ya ci gaba da cewa, ‘yan ta’addan sun fada karkashin babbar karfin wuta na sojojin, lamarin da ya tilasta musu barin sansaninsu da makamai da kayan aikinsu cikin rudani.
Wannan farmakin, a cewarsa, ya zama babban koma-baya ga ‘yan tada kayar bayan, yayin da dakarun da suka yi kaurin suna wajen fatattakar ‘yan ta’adda uku.
“Abubuwan da aka kwato sun hada da MRAP daya, motar bindiga daya, Bindigogin Dushka guda daya, Bindigogin AK 47 daya da kuma bindigar gida daya.
“Sojoji sun kuma kama Bam din Roket Propelled Grenade (RPG) guda daya, harsashi na musamman guda 273 na 7.62mm, na’urar Pumping guda daya, na’urorin Dushka 65, manyan bindigogi guda 48 da kuma babura guda uku.
“A yanzu haka dakarun soji suna amfani da nasarar da suka samu wajen fatattakar ‘yan ta’addan,” in ji shi.
Nwachukwu ya ce dakarun sojin Najeriya sun yi wani samame na daban a maboyar ‘yan ta’adda a kauyen Katakpa da ke karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa, sun yi nasarar kawar da wani mai laifi guda daya.
Ya ce sojojin sun kuma kwato bindigogin AK-47 guda biyu, bindigu mai sarrafa kansa guda daya, mujallu AK-47 guda uku da harsashi na musamman 7.62 mm har guda 90.