Rundunar ‘yan sanda a jihar Taraba ta tabbatar da mutuwar jami’inta ɗaya da kuma jikkatar wasu uku, sakamakon hatsaniyar da ta kaure tsakanin sojoji da ‘yan sanda a Jalingo babban birnin jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Usman Abdullahi Jada ne ya tabbatar wa da manema labarai hakan, jim kaɗan bayan ganawar da manyan jami’an tsaro a jihar suka yi a yau da safe.
Haɗin gwiwar jami’an tsaron jihar waɗanda suka kira taron manema labarai sun nuna takaici kan afkuwar lamarin inda suka ce za su gudanar da bincike a kai.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman ɗar-ɗar a jihar, sakamakon jinkirin da aka samu wajen bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a ƙarshe mako.