Akalla ‘yan bindiga uku ne sojojin Najeriya suka bindige a kauyen Mai-Iddo da ke karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.
Kimanin manoma hudu ne, ciki har da mace daya, aka ceto a yayin artabu tsakanin jami’an tsaro da maharan.
‘Yan ta’addan, kamar yadda Aminiya ta ruwaito, sun yi garkuwa da wasu manoma biyu a kauyen Mai-Iddo da wasu mutane biyu ciki har da wata mata a wata gona da ke kauyen Arikon da ke makwabtaka da su a makon jiya.
An tattaro cewa a ranar Lahadin da ta gabata an kubutar da wadanda harin ya rutsa da su bayan wani samame da suka kai maboyar ‘yan bindiga a wani dajin da ke kauyen Kurmin-Kare.
Rahotanni sun bayyana cewa, sojojin da ke aikin share fage a kusa da kauyukan da ke makwabtaka da karamar hukumar Kagarko, sun ci karo da mataimakan, inda suka yi artabu da ‘yan fashin guda uku.
Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ya ci tura a halin yanzu, domin kuwa ba a samu jin ta bakin kakakinta ASP Hassan Mansur ba.