A wani yanayi mai kama da zaman tankiya tsakanin jami’an soji da na ƴansanda a ƙasar nan, wani soja ya harbe wani DPO na ’yansanda a jihar Zamfara.
Al’amarin dai ya faru ne a garin Ɗanmarke da ke karƙashin ƙaramar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara a ranar Larabar nan da daddare, kamar yadda wata sanarwa da rundunar ƴansandan jihar ta Zamfara ta fitar.
SP Halliru Liman wanda shi ne DPO na Wasugu da ke jihar Kebbi ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsa ta halartar taronsu na wata-wata, inda sojoji suka tsayar da shi a wani shingen bincike.
“Duk da cewa ya bayyana musu cewa shi ɗansanda kamar yadda suka buƙata amma kuma sai kawai wani soja mai suna Hassan ya zaro bindiga ya harbe SP Liman a kansa abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.” In ji sanarwar.
Rundunar ƴansandan ta jihar Zamfara ta nemi da dukkan hukumomin da suke da ruwa da tsaki da su gudanar da cikakken bincike na yadda al’amarin ya faru.
“Abin da sojojin suka yi ya fito fili da irin rashin son aiki tare da sauran jami’an tsaro,” kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.