Rundunar sojoji ta ce, ta kashe ƴanbindiga da dama a wani artabu a jihar Plateau.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinta na X, ta ce dakarunta na Operation Safe Heaven ne suka samu nasarar kashe ƴanbindigar a karamar hukumar Bokkos na jihar ta Filato.
Sanarwar ta ce an kai samamen ne a ranar Alhamis a ƙauyukan Tutus da Hokk, da ke kan hanyar Plateau zuwa Nasarawa.
“Sojoji sun fafata da ƴanbindigar a ƙauyen Hokk, lamarin ya kai ga mutuwar da dama daga cikinsu. Saura kuma sun tsere zuwa cikin dazuka,” in ji sanarwar.
A wani samame na daban, sojojin sun ce sun kama wani da ake zargi da safarar makamai a yankin Daffo na karamar hukumar ta Bokkos a yammacin ranar, bayan samun bayanan sirri.
An kama mutumin ne da ake zargi yana safarar bindigogi a kan babur ɗinsa zuwa cikin daji.
Rundunar sojin ta ce tana ci gaba da tsare mutumin da kuma makamai da suka ƙwato yayin da ake ci gaba da bincike don gano sauran waɗanda ke aikata laifin.