fidelitybank

Sojoji sun gargadi masu shirin yin zanga-zanga a kasar nan

Date:

Shalkwatar tsaro ta gargaɗi masu shirin shirya zanga-zanga tsadar rayuwa a faɗin ƙasar da su guji jefa ƙasar cikin ruɗani.

Cikin wata sanarwa daraktan yaɗa labaran ma’aikatar tsaron ƙasar, Manjo Janar Edward Buba, ya fitar ya ce duk da cewa ‘yan ƙasar na da ‘yancin gudanar da zanga-zangar, rundunar tsaron ƙasar ba za ta lamunci tayar da fitina a ƙasar ba.

Ya ce rundunar ta fahimci masu shirya zanga-zangar na yunƙurin kwaikwayar abin da ya faru a Kenya, inda zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali.

”Kodayake ‘yan Najeriya na da ‘yancin bayyana abin da ke damunsu, sojoji ba za su lamunci duk wani abu da zai iya janyo tashin hankali a ƙasar nan da sunan zanga-zanga ba”, in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa, sojojin sun bankaɗo shirin wasu ‘ɓata-gari’ da ke ƙoƙarin amfani da zanga-zangar wajen farmakar ‘yan ƙasar da ba su ji ba su gani ba.

“Yayin da ‘yan ƙasa ke da ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana, ba su da hujjar shirya wani abu da ka iya tayar da tarzoma ko aikata laifuka”, in ji Manjo Janar Buba.

“Mun dai ga abin da ya faru a Kenya, inda wasu ɓata-gari suka mayar da zanga-zangar lumana zuwa tashin hankali, wanda kuma aka kasa magancewa”, in ji shi.

Ya ce sojojin ƙasar sun sha zuwa ayyukan wanzar da zaman lafiya a ƙasashe makwabta musamman ƙarƙashin shirin samar da tsaro na yammacin Afirka, ECOMOG, kuma sun san yadda al’umomin ƙasashen ke faɗawa cikin mawuyacin hali sakamakon tashe-tashen hankulan, don haka ba su so hakan ta faru a Najeriya ba.

bbc news nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp